logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta tabbatar da ficewar Sinawa daga Gaza

2023-11-14 22:15:10 CMG

A yau Talata ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta tabbatar da ficewar dukkanin Sinawa daga zirin Gaza lami lafiya.

Mai magana da yawun ma’aikatar Mao Ning, ta tabbatar da ficewar ‘yan  kasar ta Sin daga Gaza, yayin taron manema labarai da aka gudanar, ba tare da bayyana adadin su ba.