logo

HAUSA

Xi Jinping ya tashi zuwa kasar Amurka domin halartar taron shugabannin kasashen Sin da Amurka da taron APEC karo na 30

2023-11-14 20:01:11 CMG Hausa

A yammacin yau Talata 14 ga wata, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing zuwa birnin San Francisco na kasar Amurka domin halartar taron shugabannin kasashen Sin da Amurka, kana da halartar taron shugabannin APEC karo na 30. (Mai fassara: Bilkisu Xin)