logo

HAUSA

Kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun samu ci gaba a cikin watanni tara na farkon bana

2023-11-13 15:59:28 CMG Hausa

Wani jami'in hukumar kula da tsarin tattalin arzikin kasar Sin ya shaida wa taron tattaunawa na tattalin arziki na kasar Sin wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya karbi bakunci cewa, a cikin watanni 9 na farkon shekarar 2023, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun samu ci gaba, yayin da sashen na tattalin arzikin ke farfadowa.

Wei Dong, shugaban ofishin raya tattalin arzikin kamfanoni masu zaman kansu karkashin kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin watanni 9 na farkon bana, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun samu saurin ci gaba a fannin zuba jarin masana'antu, sun kuma samar da kayayyakin masana'antu yadda ya kamata, tare da samu saurin fadada cinikayyar kasashen waje.

Wei ya ce, yawan darajar kayayyakin da manyan kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin ke samar wa ya karu da kashi 3.3 cikin dari a watan Satumba idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara, wanda ya kusan yi daidai da karuwar kashi 3.4 cikin dari da aka samu a watan Agusta. (Yahaya)