logo

HAUSA

Sana’ar samar da sabbin kayayyakin masana’antu na kasar Sin ta shiga wani lokaci na samun saurin bunkasuwa

2023-11-13 13:37:10 CMG Hausa

Sabbin bayanai da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar a baya-bayan nan sun nuna cewa, tun daga farkon wannan shekarar da muke ciki, sana’ar samar da sabbin kayayyakin masana’antu ta kasar Sin ta ci gaba da fadada, karfinta na kirkire-kirkire yana ci gaba da inganta, yayin da ta shiga wani lokaci na samun saurin cigaba.

A cikin watanni 9 na farkon wannan shekarar, jimilar adadin sana’ar samar da sabbin kayayyakin masana’antu ta kasar Sin ta zarce yuan triliyan 5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 686, wanda saurin karuwarta ya zarce kashi goma bisa dari. Kana karfin sana’ar na kirkire-kirkire na ci gaba da ingantuwa, inda Sin ta kafa cibiyoyin kirkire-kirkire na kasa guda 7 a fannin samar da sabbin kayayyakin masana’antu, da kuma gina muhimman dandamalin ba da hidima guda 35, lamarin da ya sa cikakken tsarin samar da goyon baya ga ayyukan kirkire-kirkire ya kafu.  

Haka kuma, ma'aikatar ta bayyana cewa, karfin kamfanonin samar da sabbin kayayyakin masana’antu na kasar Sin yana karuwa sannu a hankali. A halin yanzu, yawan kamfanonin da yawan kudin shiga da suke samu ya zarce Yuan miliyan 20 a ko wace shekara ya zarce dubu 20, yayin da yawan kamfanonin da suka zama zakaru wajen samar da wani bangaren masana’antu ya kai fiye da 200. Bugu da kari, an samu manyan rukunonin masana’antu na kasa guda 7 a fannin samar da sabbin kayayyakin, wadanda suka zama "jigogi" na sa kaimi ga cigaban tattalin arzikin yankuna daban daban na Sin. (Yahaya)