logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a zirin Gaza

2023-11-13 21:08:47 CMG

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a zirin Gaza, domin baiwa fararen hula kariya, tare da fadada samar da tallafi ga mabukata, a gabar da yanayin jin kai ke kara ta’azzara.

Da take martani game da tambayoyin da aka yi mata, dangane da hare-hare kan cibiyoyin kiwon lafiya dake wuraren da ake dauki ba dadi a Litinin din nan, mai magana da yawun ma’aikatar Mao Ning, ta ce ya kamata sassan masu ruwa da tsaki, da gamayyar kasashen duniya su dauki kwararan matakai, da kara azamar kawo karshen tashin hankalin dake wakana.  (Saminu Alhassan)