logo

HAUSA

Kashi na 4 na tawagar wanzar da zaman lafiya ta jirgi mai saukar ungulu na kasar Sin za ta tafi Abyei a karshen wata

2023-11-13 10:04:20 CMG Hausa

A baya-bayan nan ne aka gudanar da bikin rantsuwa na kashi na 4 na tawagar jami’an wanzar da zaman lafiya na jirgi mai saukar ungulu na kasar Sin, da za a tura yankin musamman na Abyei.

An samar da wannan tawaga ne daga runduna ta 83 ta rundunar sojin kasar Sin PLA, kuma jami’an za su tashi zuwa Abyei cikin rukunoni biyu a karshen wannan wata. A cikin shekara mai zuwa, tawagar na da nauyin gudanar da ayyuka 17, ciki har da tura dakaru domin aikin bincike da ceto, karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Abyei. (Fa’iza Mustapha)