logo

HAUSA

Kasar Sin ba ta neman sauya Amurka haka nan bai kamata Amurka ta nemi sarrafa ko canza kasar Sin ba

2023-11-13 20:06:28 CMG Hausa

A yayin da take tsokaci game da ganawar da shugabannin kasashen Sin da Amurka za su yi, a gun taron manema labaru da aka saba yi na yau Litinin, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce kasar Sin ba ta da niyyar sauya kasar Amurka, haka kuma, bai kamata Amurkan ta rika yunkurin sarrafa, ko sauya kasar Sin ba.

Kafin hakan, a ranar Juma’ar makon jiya, wani babban jami'in kwamitin tsaron kasa a fadar White House ta Amurka da ba a bayyana sunansa ba, ya ce makasudin wannan ganawa tsakanin shugabannin kasashen Amurka da Sin shi ne, shawo kan gasa, da hana afkuwar rikici, da tabbatar da yin mu’amala yadda ya kamata.

A cewarsa, yunkurin da Amurka ke yi na sarrafa, ko canza kasar Sin cikin 'yan shekarun da suka gabata ya ci tura, kuma Amurka za ta bayyana damuwarta ga kasar Sin, kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da ma wadanda ke jawo hankulansu duka.

Dangane da hakan, kakakin ta bayyana cewa, gasar da ake yi tsakanin manyan kasashen duniya ba ta dace da halin da ake ciki a wannan zamani ba, kuma ba za ta iya warware matsalolin da Amurka ke da su, da kalubalen da duniya ke fuskanta ba.

Bugu da kari, Kasar Sin ba ta tsoron gasa, amma tana adawa da yin amfani da kalmar gasa wajen fayyace dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Game da batun damuwar sassan kuwa, kamata ya yi Amurka ta mutunta halastacciyar damuwar kasar Sin, da hakkokinta na neman ci gaba, maimakon kara jaddada damuwar Amurka, da kuma cutar da muradun kasar Sin. Kokarin sarrafa wasu kasashe bisa manufar wata kasa, da kuma tsarinta, wani nau'i ne na nuna danniya ko babakere, kuma hakan ba zai yi nasara ba.

Kwanan baya, an gudanar da kade-kade, na tunawa da cika shekaru 50 da ziyarar kungiyar kade-kaden Symphony ta Philadelphia ta Amurka a kasar Sin. Game da haka, jami’ar ta taya murna da samun nasarar karbar bakuncin bikin, tana mai cewa, kasar Sin tana farin cikin ganin an zurfafa, da fadada mu'amalar al'adu tsakanin ta da Amurka, da bude karin babuka na sada zumunci, domin sa kaimi ga fahimtar juna, da dankon zumunci tsakanin al'ummun kasashen biyu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)