logo

HAUSA

Rundunar ’yan sandan kasar Sin na neman wasu shugabannin ’yan damfara ’yan kasar Mynamar

2023-11-13 13:55:58 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da tsaron al’umma ta kasar Sin, ta ce rundunar ’yan sandan kasar na neman wasu manyan shugabanni 4 na masu aikata damfara ta wayar tarho ’yan kasar Mynamar, inda ta ce mutanen mazauna arewacin Myanmar, na kai hari kan Sinawa.

Wani bincike na hukumar tsaro ta Wenzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin ya gano cewa, bata-garin sun dade suna muggan ayyukan nasu, da suka hada da tayar da rikice-rikice da damfarar Sinawa.

Ana kuma zargin gungun mutanen da aikata manyan laifuka da dama, ciki har da kisa da raunata mutane da tsare su, lamarin dake haifar da mummunan sakamako.

A cewar ma’aikatar, bisa la’akari da cewa laifukansu a bayyane suke, kana akwai shaidu masu karfi da suka wadatar, ofishin kula da tsaro na birnin Wenzhou, ya yanke shawarar bayar da kyauta ga duk wanda ya taimaka wajen kama su. (Fa’iza Mustapha)