logo

HAUSA

Fasahar adana makamashin Sin ta kai sahun gaba a duniya

2023-11-11 15:49:17 CMG Hausa

A jiya Jumma’a 10 ga wannan wata ne aka kammala babban taron tattauna kan yadda ake adana makamashi na kasa da kasa na shekarar 2023 a birnin Ningde na lardin Fujian dake kasar Sin. Sabbin alkaluman da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa yanzu, an kafa tsarin masana’antun adana makamashi bisa mataki na farko a kasar Sin, kuma fasahar adana makamashi ta kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri, inda ta kai sahun gaba a duniya.

Sabbin alkaluma sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Satumban bana, gaba daya adadin sabbin ayyukan adana makamashin wutar lantarki na zamani da kasar Sin ta kafa ya kai KW miliyan 21.23, adadin da ya kai sahun gaba a duniya. A sa’i daya kuma, fasahar adana makamashin kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri, inda ta kai matsayin koli a duniya. (Jamila)