logo

HAUSA

Najeriya ta ce tana marhabin da gudumowar kasashen duniya domin kyautata sha`anin demokradiyyar ta.

2023-11-11 15:01:41 CGTN HAUSA

Najeriya ta ce tana marhabin da gudumowar kasashen duniya wajen kara kyautata harkokin demokradiyyar kasar ta yadda zai yi daidai da na kasashen da suka shafe karni mai yawa  kan doron siyasa.

Shugaban majalissar dattawa a tarayyar Najeriya Sanata Godswill Akpabio ne ya bukaci hakan lokacin da yake karbar bakuncin jakadan kasar Ireland a Najeriya Mr. Peter Ryan.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.