logo

HAUSA

Sin ta bukaci G7 da ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe

2023-11-10 18:53:03 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai Jumma’ar nan cewa, taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 na baya-bayan nan, ya ba da shawarar kulla alaka mai kyau da kasar Sin, ba tare da kawo cikas ga ci gaban kasar da tattalin arzikinta ba. Kasar Sin na fatan kasashe mambobin kungiyar G7 za su aiwatar da wadannan kalamai da aka ambata bisa gaskiya, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar alaka dake tsakanin sassan biyu yadda ya kamata. Kasar Sin ta bukaci kungiyar G7 da ta mutunta manufofi da ka'idojin MDD, da ka'idojin huldar kasa da kasa, da gudanar da harkokinta, tare da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe da sunan kowane dalili.

Haka kuma, Wang Wenbin ya gabatar da cewa, jiya Alhamis, babban taron MDD karo na 42 na kungiyar raya ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD, ya zartas da kudurin kafa cibiyar nazarin ilimi ta UNESCO ta kasa da kasa a birnin Shanghai na kasar Sin. Wannan shi ne karo na farko da aka kafa irin wannan cibiya a wata kasa mai tasowa, bayan Turai da Amurka. Kasar Sin ta yi maraba da amincewa da wannan kuduri, tare da nuna godiya ga UNESCO da kasashe mambobinta bisa yadda suke amincewa da kasar Sin.

A dangane da taron yanar gizo na duniya na 2023 na Wuzhen kuwa, Wang Wenbin ya bayyana cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, Wuzhen ya nuna kudiri da himmtuwar kasar Sin wajen shiga a dama da ita a tafiyar da harkokin intanet na duniya, da sa kaimi ga gina al'umma mai makomar bai daya a fannin yanar gizo. (Ibrahim)