logo

HAUSA

CIIE Ta Bude Sabbin Damammaki Na Bunkasa Harkokin Cinikayya Tsakanin Sin Da Afirka

2023-11-10 10:23:20 CMG Hausa

Wani kwararre daga kasar Ghana ya yabawa baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE), da aka kaddamar a shekarar 2018, bisa ba da damammaki masu yawa na bunkasa cinikayya tsakanin Sin da Afirka.

Paul Frimpong, babban daraktan cibiyar tsara manufofi da ba da shawarwari ta Afirka da Sin, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a cikin wata hirar da ta yi da shi a baya-bayan nan cewa, gabatar da CIIE na nuni da aniyar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen duniya baki daya domin samun nasarar hadin gwiwa tare.

A cewar Frimpong, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da ci gaban da ake samu a kullun, ya baiwa nahiyar Afirka dimbin damammaki na bunkasa harkokin cinikayya tsakanin bangarorin biyu, da kuma gaggauta bunkasa masana’antu a nahiyar.

Kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayya a Afirka cikin shekaru goma da suka gabata. Alkalumma a hukumance sun nuna cewa, hada-hadar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu ya karu da kashi 11 cikin dari zuwa dalar Amurka biliyan 282 a shekarar 2022.

Masanin ya bayyana cewa, kamfanoni daga Ghana da sauran kasashen Afirka sun fi gamsuwa da kasuwar kasar Sin mai girma fiye da kasuwannin kasashen Turai. (Muhammed Yahaya)