logo

HAUSA

Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Manufofin JKS Na Jagorancin Yankin Xizang A Sabon Zamani

2023-11-10 13:43:24 CMG Hausa

Ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani game da manufofin JKS, don gane da jagorancin yankin Xizang mai cin gashin kansa a sabon zamani.

Takardar bayanin wadda aka fitar a Juma’ar nan, mai taken "Manufofin jagorancin Xizang a sabon zamani: Matakai da nasarori" ta yi fashin baki game da ka’idojin da JKS za ta aiwatar wajen jagorantar yankin Xizang, wato yankin Tibet a sabon zamani, ta yadda za a kai ga cimma karin nasarori a dukkanin fannoni, da ma tarin nasarori da aka cimma a tarihin yankin.

Bisa wasu alkaluma da aka fitar, GDPn yankin Xizang dake kudu maso yammacin kasar Sin a shekarar 2022, ya kai darajar yuan biliyan 213.26, kwatankwacin dalar Amurka kiminin biliyan 29.7, adadin da ya ninka na shekarar 2012 da rubi 2.28.

Kaza lika takardar bayanin ta ce tsawon layin dogo da ya hade sassan yankin na Xizang ya karu daga kilomita 701 a shekarar 2012, zuwa kilomita 1,359 a shekarar 2022.

A daya bangaren kuma, takardar ta ce yankin Xizang na tabbatar da ’yancin gudanar da harkokin addinai bisa tsari, yayin da a halin da ake ciki, yankin ke da wuraren bauta na masu addinin Buddha na Tibet har 1,700, wadanda ke kunshe da malaman addinin maza da mata har 46,000. Kazalika akwai masallatai kimanin 12,000, da majami’u na katolika sama da 700.

Bugu da kari, dokokin yankin sun ba da kariya ga amfani da harshe da litattafan addinin Tibet, yayin da kuma ake ci gaba da amfani da yaren Tibet a sassa da dama da suka hada da na kiwon lafiya, da aikewa da sakwanni, da sadarwa, da sufuri, da cinikayya, da kimiyya da fasaha. Har ila yau, ana koyar da dalibai da harsuna biyu a makarantun firamare da na sakandare.  (Saminu Alhassan)