logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Kai Rangadi Kan Yadda Ake Gudanar Da Aikin Farfadowa Bayan Bala’I A Beijing Da Hebei

2023-11-10 20:29:54 CGTN HAUSA

 

Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya duba aikin farfadowa da sake ginawa bayan bala'u a birnin Beijing da lardin Hebei, inda ya jaddada cewa, ya kamata gwamnatoci na mataki daban-daban su aiwatar da umurnin kwamitin tsakiya na JKS don tabbatar da ayyukan farfadowa da tsugunar da jama’a bayan bala’u. Ya ce, dole ne a mai da bukatun jama’a a gaban kome, a kyautata karfin kandagarki da tinkarar bala’u daga indallahi.

A karshen watan Yuli zuwa farkon Agusta, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankunan Huabei da Huanghuai, abin da ya haddasa bala’in ambaliyar ruwa da bala’un da suka shafi kasa, wanda ya haddasa asarar rayuka a birnin Beijing da lardin Hebei. Xi Jinping na mai da hankali kan mutanen da bala’u ya ritsa da su, yana mai da hankali matuka kan ayyukan farfadowa bayan bala’u, ya kuma sha ba da umurni, inda ya bukaci hukumomin wurare daban-daban da su yi iyakacin kokarin ba da tabbaci ga rayukan jama’a da tsaron dukiyoyinsu, da kuma maido da zaman lafiya a yankunan da bala’in ya rutsa da su yadda ya kamata nan da nan. (Amina Xu)