logo

HAUSA

An kulla manyan yarjejeniyoyi a baje kolin CIIE

2023-11-10 19:05:59 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, an kulla yarjejeniyoyin kayayyaki da na hidimomi na tsawon shekara guda da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 78.41, yayin bikin baje kolin kayayyakin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na shida (CIIE), lamarin dake zama matsayi mafi girma.

Adadin ya nuna karuwar kashi 6.7 cikin 100 idan aka kwatanta da bikin na bara.

A daya bangaren kuma, kungiyar 'yan kasuwa ta Amurka dake birnin Shanghai (AmCham Shanghai) ta bayyana cewa, masu baje kolin kayayyakin abinci da aikin gona na Amurka sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 505 a yayin bikin baje kolin kayayyakin na CIIE.

AmCham Shanghai da ma'aikatar aikin gona ta Amurka ne suka shirya bikin sanya hannu, kuma rumfar abinci da aikin gona ta Amurka a bikin CIIE karo na 6, na zama karon farko da gwamnatin Amurka ta halarci babban taron. (Ibrahim)