logo

HAUSA

Sin na adawa da kutse ta Intanet

2023-11-09 20:25:21 CMG HAUSA

 

Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya shedawa taron manema labarai cewa, Sin ta yi suka da kakkausar murya kan duk wani nau’i na yin kutse ta yanar gizo. Ya kamata dukkan bangarorin su kiyaye tsaron hanyoyin sadarwa tare ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa, kuma kada su yi wa wasu kasashe zagon kasa ba tare da gaskiya ba.

Ya kuma nuna cewa, jiya sanarwar taron ministocin harkokin wajen kasashen G7, ta yi magana kan halin da ake ciki a tsakanin Falasdinu da Isra'ila, amma ba ta ambaci batun tsagaita bude wuta, da kawo karshen yaki, da sake dawo da shawarwarin zaman lafiya, ko aiwatar da kudurori na gaggawa da babban taron MDD ya gabatar, da ingiza kwamitin sulhu na MDD da ya dauki matakin da ya dace ba. Shin ko irin wannan sanarwa za ta taka rawa wajen kwantar da halin da ake ciki a wurin ko farfado da zaman lafiya?

Wang Wenbin ya jaddada cewa, yana fatan kungiyar G7 za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka, ba tare da nuna son kai ba, da kuma mai da martani ga kakkausar murya na kasashen duniya, da kuma daukar matakai na zahiri cikin sauri don tsagaita bude wuta da yaki, da kuma kare fararen hula. (Amina Xu)