logo

HAUSA

Sin na da mutane sama da miliyan 364 dake amfani da hidimomin kiwon lafiya ta yanar gizo

2023-11-09 10:04:24 CMG Hausa

Wani rahoton da aka fitar a jiya Laraba, ya bayyana cewa mutane sama da miliyan 364 dake kasar Sin, na amfani da hidimomin kiwon lafiya ta yanar gizo. 

Rahoton na shekarar 2023 mai taken “Ci gaban amfani da yanar gizo”, wanda cibiyar nazarin ayyukan yanar gizo ta kasar Sin ta fitar, yayin babban dandalin yanar gizo na kasa da kasa na Wuzhen na bana ko WIC, ya kara da cewa, hidimomin yanar gizo sun karade kaso 60.5 bisa dari na yankunan karkarar kasar Sin, yayin da a duk shekara, masu bukata ta musamman 68,000 ke samun ayyukan yi ta yanar gizo a kasar, lamarin dake nuni ga yadda fasahohin sadarwa ke taka rawar gani wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar Sin. 

Kaza lika, yayin dandalin na WIC na bana, an fitar da rahoton ci gaban yanar gizo na duniya na bana, wanda a cikinsa an bayyana irin gudummawar da kasar Sin ke bayarwa, wajen inganta fannonin ba da hidimomi ta yanar gizo, yayin da kuma kasar ke shiga a dama da ita wajen hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa a fannin yaki da talauci, ta amfani da fasahohin sadarwa, tana kuma raba kwarewarta ta dandali daban daban, kamar na hadin gwiwar raya tattalin arzikin Asiya da yankin Pacific. (Saminu Alhassan)