logo

HAUSA

Bankin jama'ar Sin: Fasahar kudin Sin na sahun gaba a duniya

2023-11-09 20:12:52 CMG Hausa

Yayin taron harkokin hada-hadar kudi na shekara-shekara na 2023, a lokaci guda kuma an gudanar da taron fasahar harkokin kudi na duniya karo na uku. Mataimakin shugaban babban bankin jama’a na kasar Sin Zhang Qingsong, ya bayyana cewa, gaba daya kasar Sin na kan gaba a fannin amfani da manhaja da fasahohi a fannin hidimomi da biyan kudi na zamani a duniya, kuma tana ci gaba da inganta samarwa da inganta fasahar hada-hadar kudi.

Zhang Qingsong ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta ci gaba da inganta tsarin manufofinta na kudi, don tallafawa sabbin fasahohi, da ci gaba da kyautata tsarin harkokin kudi ba tare da gurbata muhalli ba, da yin amfani da sabbin fasahohin sadarwa wajen samar da tsarin hada-hadar kudi mai inganci ga kananan kamfanoni, da kamfanoni masu zaman kansu, da daidaikun ‘yan kasuwa da kungiyoyin aikin gona, da kuma habaka harkokin kudi na zamani, don taimakawa jama'a da bunkasa kasuwanci, da ci gaba da samun sabbin nasarori. (Ibrahim)