logo

HAUSA

Kwamishinan cinikayya da zuba jari na Najeriya dake Shanghai ya yaba da manufofin kasar Sin na fadada bude kofa ga kasashen waje

2023-11-08 14:12:19 CMG Hausa

A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na shida wato CIIE a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda kwamishinan kula da harkokin cinikayya da zuba jari na yankin Asiya daga karamin ofishin jakadancin tarayyar Najeriya dake Shanghai, Ibrahim A. Ahmed ya yaba matuka da manufofin kasar Sin na fadada bude kofa ga kasashen waje, da kara shigo da kayayyaki daga kasashe daban-daban.

Wakilinmu Murtala Zhang dauke da karin bayani daga Shanghai.

Malam Ibrahim Ahmed ya ce, Najeriya na farin-cikin samun damar halartar bikin CIIE a wannan karo, ganin yadda yake samar da muhimmiyar dama ga tallata kayayyakin kasar, musamman amfanin gona da albarkatun kasa, inda ya ce:

“Tun fara bikin na bana, mutane da yawa sun zo nan don tambayar kayayyakinmu har sun yi odar wasu da dama. Mutane suna sha’awar kayayyakin Najeriya, wadanda suka bambanta da na sauran kasashen Afirka sosai. Kayayyakin Najeriya na da inganci sosai, kuma ina matukar farin-cikin ganin cewa suna samun karbuwa a wajen mutanen China.” 

Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta taba barin kasashen Afirka a baya ba wajen samar da ci gaba, ganin yadda bikin CIIE din ke samar da wata muhimmiyar dama ga kasashen Afirka wajen raya harkokin kasuwanci.

 (Murtala Zhang)