logo

HAUSA

Masana sun tattauna hanyoyin zamanantarwa a kasashe masu tasowa

2023-11-08 20:12:49 CMG Hausa

A yau ne, masana da shehunan malamai daga kasar Sin da na ketare, suka hallara a wani dandalin tattaunawa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda suka tattauna hanyoyin zamanantarwa a kasashe masu tasowa.

Sama da jami'an gwamnati 100 da masana da shehunan malamai daga kasashen Amurka, da Birtaniya, da Brazil, da Habasha da sauran kasashe, gami da masana harkokin cikin gida na kasar Sin ne, suka halarci taron tattaunawa karo na 4 na dandalin tattaunawa kan harkokin tafiyar da mulkin kasa a kasashe masu tasowa.

Sun amince cewa, zamanantar da kasar Sin hanya ce da ta dace, wadda ke bukatar hadin gwiwar samun nasara tare, da samar da wani sabon zabi, kana wani muhimmin karfi na zamanantar da kasashe masu tasowa. (Ibrahim)