logo

HAUSA

Ganawar shugabannin Sin da Australia ta share fagen kyautata dangantaka

2023-11-08 13:42:02 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan Australia Anthony Albanese wanda ya yi ziyarar aiki a Sin. Yayin zantawar shugabannin 2 a ranar Litinin a birnin Beijing, Xi ya jaddada bukatar hadin gwiwar sassan biyu, ta yadda za su gina kyakkyawar alaka bisa daidaito, da cimma matsaya, da kawar da sabani, da hadin gwiwar cimma moriya tsakaninsu. 

A nasa tsokacin kuwa, firaminista Albanese ya ce Australia da Sin na da banbanci ta fuskar tsarin siyasa, kuma hakan ba wata matsala ba ce, sai dai bai dace a bari sabanin ya gurgunta yanayin dangantakar sassan biyu ba. Ya ce tattaunawa da hadin gwiwa ne zabin da ya dace Australia da Sin su runguma.

Wannan ne dai karon farko da wani firaministan Australia ya ziyarci kasar Sin cikin shekaru 7 da suka gabata. Kaza lika alakar Sin da Australia na cikin muhimman manufofin kasar Sin game da kasashen yamma masu ci gaba. A matsayinta na babbar abokiyar huldar cinikayyar Australia, sauye-sauye, da bude kofa, da zamanantarwa da Sin ke aiwatarwa na ingiza samuwar damammaki masu tarin yawa ga Australia. 

To sai dai kuma duk da haka, a zamanin gwamnatocin Australia biyu da suka gabata, kasar ta rungumi manufar nan ta Amurka mai lakabin "Indo-Pacific strategy", wadda a karkashinta aka hana karbar fasahar 5G ta kamfanin Huawei, kana aka rika takalar kasar Sin ta fakewa da batutuwa kamar na jihar Xinjiang da tekun kudancin Sin, wanda hakan ya kai ga haifar da koma baya ga dangantakar dake tsakanin Sin da Australia, tare da illata moriyar Australia.

A watan Nuwanban shekarar bara ne kuma, a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, shugaba Xi ya gana da mista Albanese wanda jim kadan da kama aikin firaministan kasar Australiya, ya kuma share fagen farfadowa, da kuma inganta alakar Sin da kasarsa. Yayin ganawarsu ta wannan karo a birnin Beijing kuma, bangaren Sin ya jaddada bukatar lura matuka, da nuna adawa da manufofin dake yunkurin jefa yankin Asiya da Pacific cikin rudani, kana ya nuna dalilin da ya sa alakar Sin da Australia ta shiga mawuyacin hali a ’yan shekarun baya.

Alakar Sin da Australia, wadda ta ci karo da koma baya, a yanzu tana farfadowa cikin kuzari. Kaza lika ana fatan Sin da Australia za su rungumi yanayin zamanin da ake ciki, su kyautata fahimtar juna, da amincewar juna ta hanyar zaman jituwa, kana su cimma bunkasuwar bai daya ta hanyar hadin gwiwar cimma moriya tare. (Saminu Alhassan)