logo

HAUSA

Fiye Da 90% Na Wadanda Suka Ba Da Amsa A Wani Binciken Da Aka Gudanar Sun Yi Imanin Cewa CIIE Na Kara Kuzari Kan Tattalin Arzikin Duniya

2023-11-08 11:21:27 CMG Hausa

Sakamakon wani kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta intanet da CGTN ta gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa, sama da kashi 90 cikin kashi 100 na masu bayyana ra’ayi sun yi imanin cewa, taron baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) da kasar Sin ta shirya a cikin shekaru 6 da suka gabata, ya nuna wata alama mai karfi na ci gaba da bude kofar Sin ga kasashen duniya, lamarin da ya zama muhimmiyar dama ga duniya mai cike da rikice-rikice da tattalin arzikin duniya mai raunin farfadowa.

An fitar da binciken ne a kafafen yada labarai na CGTN cikin harsunan Turanci da Spanisanci da Faransanci da Larabci da kuma Rashanci, inda sama da masu amfani da yanar gizo 10,000 suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24.

A cikin binciken, kimanin kashi 83.6 cikin kashi 100 na masu bayyana ra’ayi a duniya sun yi imanin cewa, shaharar CIIE ya nuna kwarin gwiwar kasuwancin duniya ga yin ciniki cikin 'yanci da bude kasuwanni, yayin da wasu 86.8 cikin kashi 100 sun yi imanin cewa, CIIE ya zama muhimmin dandali ga kamfanoni don samun tabbaci a cikin yanayin rashin tabbaci na duniya. (Yahaya)