logo

HAUSA

Takardun iznin mallakar fasaha da Sin ta gabatar na matsayin farko a duniya a 2022

2023-11-08 19:41:16 CMG Hausa

Mai magana da yawuun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jagoranci taron manema labarai da aka saba gudanarwa Larabar nan. Kuma wani dan jarida ya yi tambaya cewa, kwanan nan, hukumar kare ‘yancin mallakar fasaha ta duniya ta fitar da "Rahoton alkaluman mallakar fasaha na duniya", inda ta bayyana cewa, kasar Sin ce ta fi yawan masu neman mallakar fasaha a shekarar 2022. Mene ne ra’ayin kasar Sin kan wannan batu?

Wang Wenbin ya bayyana cewa, mun lura da rahotannin da abin ya shafa. Rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2022, kasar Sin ta gabatar da takardar neman iznin mallakar fasaha kusan miliyan 1.6, wadda ta zo ta daya a duniya. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, ya zuwa watan Yunin bana, adadin fasahohin kirkire-kirkire masu inganci a kasar Sin ya kai miliyan 4.568, wanda kuma ya zama na daya a duniya baki daya. Kasar Sin tana matsayi na 12 a fannin kididdigar kirkire-kirkire ta duniya a shekarar 2023, inda ta samu maki 6 a matsayi na daya a duniya. Wannan ya nuna gagarumar nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin mallakar fasaha. (Ibrahim)