logo

HAUSA

Xi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Kasa Da Kasa Na Wuzhen Kan Intanet

2023-11-08 13:39:09 CMG Hausa

A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabin bude taron kasa da kasa na Wuzhen kan kafar intanet.

Cikin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, Xi Jinping ya jaddada bukatar kasa da kasa su zurfafa musaya da hadin gwiwa a aikace, domin daukaka gina al'umma mai makoma ta bai daya a bangaren kafar intanet, zuwa wani sabon mataki.

Ya kara da kira da a ba da fifiko ga samar da ci gaban kafar intanet domin karin kasashe da jama'ar duniya su ci gajiyarsa.

Yayin da yake kira da a samar da kafar intanet mai karin tsaro da aminci, ya ce akwai bukatar girmama 'yancin da kasashe ke da shi kan kafarsu ta intanet da kuma yadda ko wace kasa ke son tafiyar da harkokin bangaren. Haka kuma, a yi adawa da masu neman babakere da fito-na-fito da gasar mallakar makamai a kafar intanet. (Fa'iza Mustapha)