logo

HAUSA

Sin za ta ci gaba da taka rawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra'ila

2023-11-07 19:05:11 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru Talatar nan cewa, a matsayinta na shugabar karba-karba ta kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa, wajen sa kaimi ga kwamitin sulhu na MDD, wajen daukar matakan da suka dace na tsagaita bude wuta, da kawo karshen yaki, da rage yanayin jin kai da ake ciki, da taka rawar da ta dace wajen samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Falasdinu da Isra'ila ta hanyar "shirin kafa kasashe biyu".

Ya ce, wajibi ne kasashen duniya su dauki matakin gaggawa, kuma kasashen dake wajen yankin, musamman ma manyan kasashe, su tabbatar da gaskiya da adalci, tare da taka rawa mai ma'ana wajen ganin an sassauta yanayin da ake ciki.

Bugu da kari, ya ce maganar da ake cewa, wai kasar Sin tana haifar da "tarkon bashi" wani zance ne kawai da wasu makiya ke kirkira don neman yin katsalandan da kuma gurgunta hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa, kuma wannan hujjar ta sabawa fahimtar tattalin arziki. (Ibrahim)