logo

HAUSA

An fitar da gargadin zubar dusar kankara da iskar hunturu a sassan arewa maso gabashin kasar Sin

2023-11-07 11:24:02 CMG Hausa

Cibiyar hasashen yanayi ta kasar Sin, ta fitar da gargadi mataki na 2 mafi tsanani na hunturu wato mai launin lemo, wanda ke nuni ga yanayin zubar dusar kankara da iska mai sanyi, a lardunan arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar da cibiyar ta fitar da yammacin jiya Litinin, ta ce tun daga karfe 8 na dare jiya zuwa 8 na daren Talatar nan, lardunan Jilin da Heilongjiang za su fuskanci yanayi na zubar dusar kankara. Kaza lika, wasu sassan lardin Heilongjiang za su fuskanci zubar kankara da iska mai matukar sanyi, lamarin da zai kai tsayin dusar kankara a wasu sassan lardin zuwa sama da santimita 12. Don haka cibiyar ta shawarci mahukuntan yankunan da su kimtsawa wannan yanayi.

Kasar Sin na da launukan gargadi na yanayin hunturu guda 4 gwargwadon tsananin yanayin, wadanda suka hada da launin ja mai nuni ga kololuwar matsayin hunturu, sa launin lemo a mataki na 2, akwai kuma launin dorawa a matsayi na 3, yayin da launin shudi ke wakiltar matsayi mafi sauki na yanayin hunturu.  (Saminu Alhassan)