logo

HAUSA

Ana sa ran kasashe 5 manyan baki a bikin CIIE za su samu damarmakin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da kasar Sin

2023-11-07 11:11:24 CMG Hausa

A bana, an dawo da gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin CIIE a zahiri, inda aka kebe yankunan musamman ga kasashe 69 da hukumomin kasa da kasa 3 don su nuna kayayyakinsu, lamarin da ya sa za su ci gajiyar bude kofar kasar Sin da hadin gwiwa da ma damarmakin dake kasuwannin kasar, cikinsu har da Vietnam da Afrika ta Kudu da Kazakhastan da Serbia da Honduras, a matsayin manyan baki.

Afrika ta Kudu ta halarci bikin CIIE shekaru 5 a jere. A shekarun baya-bayan nan, ana ganin karin abincin kasar Afrika ta Kudu a teburin abincin Sinawa, kuma baje kolin CIIE ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa fitar da kayayyakin musamman na Afrita ta Kudu zuwa kasar Sin, lamarin da ya samar da muhimmiyar dama ga ‘yan kasuwar kasar na kara shiga kasuwar kasar Sin.

Zanele Mkhize, daraktar sashen talla da fitar da kayayyaki ta hukumar bunkasa cinikayya da zuba jari ta Afrika ta Kudu, ta ce dangantakar kasarta da Sin dangantaka ce irin ta moriyar juna, inda dukkan bangarorin ke samun nasara da amfanawa al’ummominsu. Ta ce dangantaka irin wannan, tana da kyau ga makomar kasashen biyu da ma ta duniya, domin tana haifar da alfanu ga kowa da kowa dake cikinta. (Fa’iza Mustapha)