logo

HAUSA

Sin ta ba da shawarar yin hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha

2023-11-07 21:29:20 CMG Hausa

  

A karon farko kasar Sin ta gabatar da shawarar yin hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha tsakanin kasashen duniya, a yayin taron musayar fasahohin kimiyya da fasaha kan shawarar ziri daya da hanya daya da aka bude a birnin Chongqing dake yankin kudu maso yammacin kasar Sin jiya Litinin.

Shawarar ta bukaci bayar da shawarwari da aiwatar da manufar hadin gwiwar bude kofa ga kasashen duniya a fannin kimiyya da fasaha, da bin ka'idar cewa "kimiyya ba ta da iyaka kuma tana amfanar daukacin bil-Adama", kana a hada kai don gina al'ummar duniya a fannin kimiyya da fasaha. (Ibrahim)