logo

HAUSA

Dandalin Hongqiao na maida hankali ga kiyaye tsarin cinikayyar sassa daban daban

2023-11-07 15:40:14 CMG

A jiya Litinin ne aka gudanar da karamin dandali, mai taken kiyaye tsarin cinikayyar sassa daban daban da inganta tattalin arzikin duniya, karkashin dandalin tattauna tattalin arziki na duniya na “Hongqiao”.

Yayin zaman dandalin na jiya, jagororin sa sun amince cewa a shekarun baya bayan nan, ana fuskantar karin barazanar turka turkar cinikayya, wanda hakan ya zamo babban kalubale ga bunkasar tattalin arzikin duniya.

Game da hakan, mataimakin ministan cinikayyar kasar Sin Ling Ji, ya ce a shekarun baya bayan nan, kebe kai, da kariyar ciniki na karuwa, don haka kamata ya yi tsarin cinikayya tsakanin sassa daban daban ya warware wannan matsala. Ya ce kasar Sin ta rungumi manufar bude kofa, kuma za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an aiwatar da tsarin cinikayya tsakanin sassa daban daban yadda ya kamata, wanda ke da kungiyar cinikayya ta duniya WTO a matsayin jigonsa.

Har ila yau, Sin za ta kara inganta tsarin kasa na shiga a dama da ita wajen aiwatar da sauye sauye a kungiyar WTO, da cimma matsaya guda ta aiwatar da sauye sauyen tare da sauran mambobin kungiyar, ta hanyar kawar da banbance banbance gefe guda.

Mahalarta dandalin dai sun amince cewa, daidaito da wanzar da ci gaban tattalin arzikin duniya za su samu ne kadai ta hanyar karfafa hadin gwiwa, da ingiza kirkire-kirkire. (Saminu Alhassan)