logo

HAUSA

Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Farko Na Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Kan Musayar Kimiyya Da Fasaha

2023-11-06 15:10:13 CMG Hausa

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron shawarar “ziri daya da hanya daya” kan musayar kimiyya da fasaha na farko da aka bude a birnin Chongqing na kudu maso yammacin kasar Sin.

A cikin wasikar tasa, ya bayyana cewa, an yi nasarar gudanar da dandalin hadin gwiwar kasa da kasa na shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku, wanda ya haifar da wani sabon mataki na ci gaba mai inganci ga shawarar “ziri daya da hanya daya”, wanda hadin gwiwar kimiyya da fasaha ya kasance muhimmin bangare.

Xi Jinping ya ce, "Kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga ruhin hanyar siliki bisa zaman lafiya da hadin gwiwa, tare da gaskiya da fahimtar juna, da samun moriyar juna, da aiwatar da cikakken shirin hadin gwiwa na kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, da sa kaimi ga yin mu'amalar kirkire-kirkire na kasa da kasa." 

Ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen samar da damar samun bunkasuwar kirkire-kirkire, da ba da damar yin hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire, da karfafa hadin gwiwar kirkire-kirkire, da sa kaimi ga cimma nasarar kirkire-kirkire, don amfanar da jama'a daga dukkan kasashen duniya, ta yadda za su ba da gudummawa mai inganci ga ci gaban shawarar “ziri daya da hanya” da gina al'umma mai makomar bai daya ga bil'adama. (Muhammed Yahaya)