logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya bukaci a kara azama wajen gina kasar Sin mai kwanciyar hankali

2023-11-06 15:56:42 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci a ba da gagarumar gudummawar daga matsayin manufar gina kasar Sin mai kwanciyar hankali.

Shugaba Xi ya yi kiran ne a Litinin din nan a birnin Beijing, lokacin da yake zantawa da wakilan sassan da suka rungumi tafiyar "Fengqiao model", mai rajin ingiza kyakkyawan jagoranci a matakin farko na al’ummun kasa.

Xi ya karfafawa wakilin gwiwar ci gaba da aiki, da zurfafa manufar "Fengqiao model", ta yadda za a bunkasa kyakkyawan jagoranci a sabon zamani.

An kafa wannan tafiya ta Fengqiao ne a lardin Zhejiang shekaru 60 da suka gabata, kuma manufar ta shahara wajen dogaro da al’umma wajen warware rigingimu a matakin farko na zamantakewa. Kuma tun daga lokacin ne ake ta daga matsayin manufar zuwa dukkanin sassan kasar Sin. 

Tun lokacin babban taron wakilan JKS karo na 18 da ya gudana a shekarar 2012, shugaba Xi ya gabatar da muhimman umarni, game da aiwatarwa da kara bunkasa manufar “Fengqiao model”. (Saminu Alhassan)