logo

HAUSA

Sin na adawa da matakin Amurka na neman sanyawa wasu hukumominta takunkumi

2023-11-06 19:52:30 CMG Hausa

Dangane da sanarwar baya bayan nan da sashen baitulmalin Amurka ya bayar cewa, za a sanya wasu hukumomin kasar Sin cikin “Jerin sunayen hukumomin da aka kebe na musamman” ta hanyar fakewa da wai dalilan hada kai da Rasha, mai magana da yawun ma’aikatar cinikayyar Sin, ya mayar da martani Litinin din nan cewa, kasar Sin ta lura da yanayin da ake ciki kan wannan batu.

Ya ce matakin Amurka kan wannan lamari, wani nau'in takunkumi ne na kashin kai da kuma “ikon nuna fin karfi”, wanda ke lalata tsarin kasuwanci da ka’idoji na kasa da kasa, kuma yana shafar tsaro da kwanciyar hankalin masana’antu da ma tsarin samar da kayayyaki. Kasar Sin ba ta gamsu da hakan ba, kuma tana adawa da shi. (Ibrahim)