logo

HAUSA

Matsayin Sin kan batun Falasdinu a bayyane yake

2023-11-06 19:12:38 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labarai Litinin din nan cewa, matsayin kasar Sin kan batun Palasdinu a ko da yaushe a bayyane yake. Kasar Sin tana ba da shawarar kafa kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci bisa kudurorin MDD mafiya dacewa, kuma za ta ci gaba da yin aiki tukuru tare da ragowar kasashen duniya har ganin an kai ga cimma wannan mataki.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, a matsayinta na shugabar karba-karba ta kwamitin sulhu, kasar Sin za ta yi kokarin ganin an dawo da zaman lafiya a Palasdinu, da sa kaimi ga kwamitin sulhu don sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, tare da taka rawar da ya dace, da kawar da rikicin da ake fama da shi, da ma kiyaye lafiyar fararen hula.

A game da huldar dake tsakanin kasar Sin da Amurka kuwa, Wang Wenbin ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da ba da goyon baya da karfafa mu'amala tsakanin gwamnatoci da kungiyoyin da ba na gwamanati ba. Ban da wannan kuma, kasashen Sin da Amurka za su gudanar da shawarwarin hana yaduwar makamai a matakin sassa a birnin Washington nan gaba kadan, inda za su gudanar da tattaunawa da yin mu'amala da juna kan batutuwa da dama, kamar aiwatar da yarjejeniyoyin sarrafa makamai na kasa da kasa da hana yaduwa.

Ban da wannan kuma, bisa gayyatar da kasar Amurka ta yi masa, mataimakin firaministan majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma shugaban tawagar kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, He Lifeng, zai ziyarci kasar Amurka daga ranar 8 zuwa 12 ga watan Nuwamba. (Ibrahim)