logo

HAUSA

Ministan kasuwanci: Kasar Sin za ta inganta amfani da jarin waje

2023-11-06 10:40:07 CMG Hausa

Ministan kasuwanci na kasar Sin Wang Wentao ya bayyana a jiya Lahadi a birnin Shanghai cewa, kasar Sin za ta ci gaba da inganta yadda ake amfani da jarin waje, da kuma mayar da kasar ta zama wurin da za a iya zuba jari mai dorewa.

Wang ya bayyana hakan ne a yayin taron koli na “Shekarar zuba jari a kasar Sin” da shirin bunkasa birnin Shanghai, wanda ya kasance wani muhimmin al’amari a yayin bikin baje kolin kayayyaki da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na 6. 

Wang ya ce sannu a hankali kasar za ta rage jerin sunayen cinikayya da aka haramta zuba jarin kasashen waje, da soke takunkumin hana zuba jarin waje gaba daya a fannin masana'antu, da fadada bude kofa ga masana'antun hidima na zamani.

Har ila yau, kasar Sin za ta goyi bayan yankunan cinikayya maras shinge na gwaji da yankin cinikayya maras shinge na tashar jiragen ruwan Hainan don daidaitawa da dokokin kasa da kasa, kamar Yarjejeniyar Ci Gaba Da Hadin Gwiwar Trans-Pacific da Yarjejeniyar Hadin Kan Tattalin Arziki A Yanar Gizo. Haka kuma, za a gudanar da tarurruka don warware damuwar kamfanoni, a cewar Wang. (Yahaya)