logo

HAUSA

Rahoton MDD: Yankunan cinikayya cikin ‘yanci na gwaji na Sin sun amfanawa kasashe masu tasowa

2023-11-06 19:53:15 CMG HAUSA

 

Yau Litinin, ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta gabatar da bikin ingiza zuba jari ga yankunan cinikayya cikin ‘yanci na gwaji na Sin mai taken “shekarar zuba jari ta Sin”, inda taron cinikayya da raya kasa na MDD ya gabatar da rahoto mai taken “Rawar da yankunan ciniki cikin ‘yanci na gwaji na kasar Sin suke takawa a fannin ingiza aikin yin kirkire-kirkire a fannin manufofi da yiwa sana’o’i kwaskwarima da hadin kan kasashe masu tasowa”.

Rahoton ya amince da ci gaban da wadannan yankuna ke samu a cikin shekaru 10 da suka gabata tun kafuwarsu, ya kuma nuna cewa, yankunan gwaji wani aikin da Sin ta kirkiro, wanda ya ingiza tsarin bude kofa da yin kwaskwarima da take kokarin gudanarwa. Yankunan na amfanawa wajen kyautata hidimomin gwamnati da ingiza yanayin kasuwanci, ta yadda za a sa kaimi ga yiwa sana’o’i kwaskwarima, da ciyar da karuwar jarin da ‘yan kasuwar ketare suke zubawa a Sin. Rahoton na ganin cewa, ba ma kawai yankunan sun taimakawa Sin wajen kara kulla dangantaka da tuntuba da sauran kasashe ba, har ma sun zama abin misali ga kasashe masu tasowa wadanda ke neman yin kwaskwarima da bude kofa da samun bunkasuwa. (Amina Xu)