logo

HAUSA

Xi ya aika sakon jaje ga takwaransa na Nepal bisa girgizar kasar da ta afakawa kasar

2023-11-05 15:40:55 CMG Hausa

A jiya Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika sakon jaje ga takwaransa na kasar Nepal, Ram Chandra Poudel bisa mummunan girgizar kasar da ta auku a kasar, inda Xi ya bayyana cewa, ya kadu matuka da jin labarin aukuwar girgizar kasar da ta faru a jihar Karnali dake kasar.

Xi ya kara da cewa, a madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin, yana mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu a bala’in, tare da isar da jaje ga iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka ji rauni, haka kuma yana fatan wadanda suka ji rauni za su samu sauki cikin sauri. (Jamila)