logo

HAUSA

An mika babban jirgin ruwan fasinja na farko da Sin ta kera a Shanghai

2023-11-05 19:56:19 CMG Hausa

An mika babban jirgin ruwan fasinja na farko da kasar Sin ta kera, mai suna Adora Magic City a birnin Shanghai. Jirgin mai tsayin mita 323.6 da fadin mita 37.2, zai iya daukar fasinjoji 5,246.

A ranar 1 ga Janairun shekarar 2024 ne, ake sa ran jirgin tamkar wani birni na zamani a kan teku, zai fara zirga-zirgar kasuwanci. (Ibrahim)