logo

HAUSA

An kammala bikin Canton Fair tare da kulla yarjeniyoyin da suka kai dala biliyan 22.3 a zahiri

2023-11-05 16:02:43 CMG Hausa

           

A jiya ne, aka kammala bikin baje kolin shigi da ficin kayayyaki na kasar Sin karo na 134 a birnin Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke yankin kudancin kasar, inda aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fitar da kayayyaki, da darajrsu ta kai dalar Amurka biliyan 22.3 a zahiri.

Mai Magana da yawun bikin, Xu Bing, ya bayyana cewa, darajar ta haura kashi 2.8 cikin 100, idan aka kwatanta da bikin na baya

Kamfanonin da suka halarci bikin, sun kulla yarjejeniyoyin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 12.27, tare da abokan huldar kasuwancinsu na kasashen dake raya shawarar ziri daya da hanya daya (BRI), wanda ya karu da kashi 2 cikin 100, idan aka kwatanta da na bikin shekarar da ta gabata.

Tun daga ranar Juma'a, masu sayayya na ketare daga kasashe da yankuna 229, sun halarci bikin baje kolin ta kafar intanet da kuma a zahiri. Kimanin masu sayayya dubu 198 daga ketare ne suka halarci bikin ta intanet, kashi 6.4 fiye da adadin wadanda suka halarta a bikin karo na 126 da aka gudanar a shekarar 2019.

An dai kaddamar da bikin ne a shekarar 1957, kuma ana gudanar da shi sau biyu a kowace shekara, ana kuma daukar bikin a matsayin babban ma'aunin cinikayya na kasar Sin.(Ibrahim)