logo

HAUSA

Ruto: Aikin hadin gwiwa karkashin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ya kawo babban canji ga Kenya

2023-11-04 15:58:00 CMG Hausa

Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya bayyana shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya a matsayin mai hangen nesa, wadda a karkashinta, aka samu nasarori da dama.

William Ruto, ya bayyana haka ne yayin da yake hira da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG. A cewarsa, an gabatar da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya bisa tushen fasahohin da aka samu daga hanyar siliki da aka kafa shekaru da dama da suka gabata, wato an gina hanyoyin yau da kullum kamar na motoci da hanyoyin jiragen kasa, da ayyukan sadarwa da sauransu, don sa kaimi ga bunkasa cinikayya a karni na 21. Ya kara da cewa, an raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, inda ta rikide daga tunani zuwa ayyukan samun moriya na zahiri kuma masu amfani. Alal misali, an gina hanyar jirgin kasa daga Mombasa zuwa Nairobi na kasar Kenya. Ya ce da farko a lokacin da aka fara gina hanyar, mutane da dama sun yi tsammani ba zai yiwu ba. Amma yanzu ana jigilar kayayyaki da fasinjoji a kan hanyar jirgin kasa tsakanin Mombasa da Nairobi, wanda ya kawo babban canji ga kasar Kenya.

Ban da wannan kuma, shugaba Ruto ya bayyana cewa, shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, da shawarar samun bunkasuwar duniya, da shawarar kiyaye tsaron duniya, dukkansu sun samar da gudummawa ga ci gaban duniya a fannoni daban daban. Bugu da kari ya yabawa kasar Sin, yana mai cewa, ba ta tilasta ra’ayoyinta ga sauran kasashe, kuma tana ayyukan da suka dace, lamarin da ya kai ta ga samun ci gaba. (Zainab)