logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Iyakar Kokarin Saukaka Rikicin Gaza

2023-11-04 16:11:54 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kasarsa za ta ci gaba da ingiza kwamitin sulhu na MDD wajen sauke nauyin dake wuyansa tare da zartas da kudurorin taimakawa saukaka rikicin Gaza ba tare da bata lokaci ba.

Wang Yi ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud.

Faisal Al Saud ya yabawa kasar Sin kan yadda take daukaka adalci dangane da rikicin Palasdinu da Isra’ila da kuma goyon bayan shirye-shirye da shawarwarin kasashen Larabawa.

Ya kara da yaba mata game da rawar da take takawa a matsayinta na babbar kasa, wajen ingiza kwamitin sulhu domin ya dauki mataki.

Ya ce Saudiyya na kira da a dakatar da bude wuta nan take domin tabbatar da kayayyakin agaji sun isa Gaza nan ba da jimawa ba da nufin shawo kan matsalar jin kai.

Har ila yau, Wang Yi ya ce, kudurin da aka amince da shi a makon da ya gabata da kuri’u masu rinjaye yayin taron gaggawa na musamman na babban taron MDD, ya nuna kiran kasashen duniya, kuma kasar Sin na goyon bayan kudurin.

Ya ce, a matsayinta na shugabar karba-karba na kwamitin sulhun a wannan watan, kasar Sin za ta ci gaba da yin iyakar kokarinta wajen dawo da zaman lafiya da ingiza kwamitin ya sauke nauyin dake wuyansa da cimma matsaya da kasa da kasa da zartas da kudurin nan ba da jimawa ba, domin saukaka rikicin da ake fama da shi da kare halaltattun hakkokin al’ummar Palasdinu. (Fai’za Mustapha)