logo

HAUSA

Xi Ya Tattauna Da Shugaban Gwamnatin Jamus

2023-11-03 21:08:48 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz yau Juma’a ta kafar bidiyo.

A cewar Xi Jinping, a yanzu haka, cinikayya tsakanin Sin da Jamus na samun ci gaba yadda ya kamata, kuma yawan jari a tsakaninsu ma na karuwa, baya ga dangantakarsu dake kara kyautatuwa da kara karfi da samun nasarori.

Sama da kamfanonin Jamus 130 ne za su halarci baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin CIIE karo na 6, wanda ke nuna kwarin gwiwar da kamfanonin Jamus din ke da shi kan ci gaban Sin. Ana kuma fatan bangaren Jamus zai nace ga fadada bude kofar hadin gwiwa ga kamfanonin kasar Sin.

A nasa bangare, Olaf Scholz ya bayyana ra’ayin kasarsa game da rikicin Palasdinu da Isra’ila, yana mai fatan ci gaba da tuntubar juna tsakanin Jamus da Sin kan batun.

Game da hakan, Xi Jinping ya ce idan ana son warware tushen rikicin Palasdinu da Isra’ila ko kuma rikicin Ukraine, to akwai bukatar yin tunani mai zurfi a bangaren tsaro, da nacewa ga samar da cikakken tsaro na bai daya cikin hadin gwiwa da samar da ingantaccen tsarin tsaro mai dorewa kuma bisa adalci. (Fa’iza Mustapha)