logo

HAUSA

Nasarorin da aka cimma a taron BRF ya kara nuna fa’idar hadin gwiwa da samun nasara tare

2023-10-25 19:45:15 CMG Hausa

Tun bayan da aka kammala taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRF) karo na uku a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin cikin nasara, kasashe da masana a sassa daban-daban na duniya ke bitar muhimman nasarorin da aka cimma a taron, da muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa da samun nasara tare.

Bayanai na nuna cewa, an cimma manyan nasarori kusan 458 a taron da ya samu halartar manyan shugabannin duniya da dama, wanda hakan ke nuna kyakkyawan fata da ake da shi, na hada karfi da karfe wajen bunkasa shawarar zuwa wani sabon matsayin ci gaba mai inganci.

Bugu da kari, karkashin wadannan nasarori, kasar Sin za ta aiwatar da wasu manyan tsare tsare guda 8, wanda hakan ke nuna aniyar kasar ta nacewa ga manufar bunkasa duniya da samar da wadata, da ma zamanantar da baki dayan kasashen duniya.

Kamar yadda aka saba, a karshe taron ya fitar da sanarwar shugaba, game da manyan sakamakon da aka cimma, mai kunshe da jerin takardun bayanai da ayyuka, wadanda adadin su ya kai 458. Haka kuma, kasar Sin da wasu kamfanonin ketare, sun cimma matsayar gudanar da ayyukan hadin gwiwa da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 97.2.

Wadannan nasarori sun zamo tamkar kuri’u na nuna goyon baya, da amincewar galibin abokan huldar shawarar ta Ziri Daya da Hanya Daya. Shawarar dake maraba da kowa da kowa, ba tare da nuna wani bambanci, ko gindaya wani sharadi ba.

Taron dandalin tattauna hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya karo na uku da aka gudanar, ya shaida burikan da aka sanya gaba, na hadin gwiwar sassan kasa da kasa, da bude kofa da cimma gajiya tare. (Ibrahim Yaya)