logo

HAUSA

Abun da ya faru a MDD gargadi ne ga Amurka

2023-10-20 21:23:00 CMG Hausa

A ranar Laraba 18 ga watan nan, sassan kasa da kasa sun nuna rashin gamsuwa yayin da wakilin Amurka ke jawabi a taron hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, a wani mataki na nunawa Amurkan adawar su da goyon bayan Isra’ila zalla da take yi, da watsi da batun kare hakkin Falasdinawa game da batun takaddama da Isra’ila.

Ya zuwa yanzu, dauki ba dadi tsakanin tsagin Falasdinu da Isra’ila ya haifar da rasuwar sama da mutane 5200. A kuma wannan gaba da ake fuskantar tashin hankali, kuma a matsayin Amurka na muhimmiyar mai ruwa da tsaki a rikicin, ta gaza rungumar dukkanin sassa dake fada da juna, maimakon haka ta dakile kudurin tabbatar da agajin jin kai yayin taron kwamitin tsaro na MDD har sau biyu, ta kuma zuba ido al’amura na kara tabarbarewa tsakanin Falasdinu da bangaren Isra’ila, lamarin da ya haifar da asarar rayukan dubban fararen hula.

Ya kamata Amurka ta sauke nauyin dake wuyan ta, ta yi aiki tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen ingiza matakan tsagaita wuta da kawo karshen yaki. In ba haka ba, dukkanin sassan duniya za su juya mata baya.  (Saminu Alhassan)