Ibrahim Aminu Ibrahim: Ina son harshen Sinanci sosai!
2023-10-10 15:45:57 CMG Hausa
Ibrahim Aminu Ibrahim, dan asalin Kano ne dake arewacin Najeriya, wanda ya taba karatun harshen Sinanci a wata makaranta dake garin Kwankwaso tun daga shekara ta 2015 zuwa 2020.
Kwanan nan, Murtala Zhang ya samu damar hira da shi, inda malam Ibrahim Aminu Ibrahim ya bayyana yadda ya koyi yaren Sin, da kalubale da matsalolin da yake fuskanta wajen karatun. Ya kuma bayyana wasu al’adun kasar Sin gami da halayen mutanen kasar wadanda suke burge shi.
Malam Ibrahim Aminu Ibrahim ya ce, duk da cewa ba ya karatun yaren Sin a halin yanzu, saboda karatun jami’a gami da aikin kasuwanci da yake yi, amma ba zai taba mantawa da yaren ba, kana kuma burinsa shi ne, ci gaba da kara ilimi game da yaren. (Murtala Zhang)