logo

HAUSA

Antonio Guterres: A kawo karshen yawan tashe-tashen hankula a gabas ta tsakiya

2023-10-10 09:45:42 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kawo karshen yawan tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya, a gabar da rikicin Isra’ila da Falasdinu ya sabbaba kisan sama da mutum 1600.

Mista Guterres, wanda ya yi kiran cikin wata sanarwa a jiya Litinin, ya ce rikicin sassan biyu na wannan karo yana da tushe, duba da cewa wutarsa ta ruru ne sannu a hankali, sakamakon tsawon lokaci da sassan biyu suka shafe suna sa-in-sa, kana an shafe shekaru 56 ana mamayar yankuna, ba tare da samar da wani sahihin tsari na siyasa domin warware takaddamar ba.

Babban jami’in na MDD ya kara da cewa, ya zama wajibi Isra’ila ta cimma burinta na wanzar da tsaro bisa doka, yayin da a daya hannun ya zama tilas su ma al’ummar Falasdinawa su tabbatar da ganin tsari na gaskiya na kafuwar kasarsu.

Ya ce ta hanyar shawarwarin zaman lafiya na hakika ne kadai za a iya cimma halastattun burikan sassan biyu, kuma karkashin manufofin samar da tsaron sassan biyu, da burin kafuwar kasashe biyu masu cin gashin kai, daidai da kudurorin MDD, da dokokin kasa da kasa, da yarjejeniyoyin da aka amince a baya ne za a iya wanzar da daidaito mai dorewa a wannan yanki, da ma sauran sassan gabas ta tsakiya.

Ya zuwa safiyar Talatar nan, ana ci gaba da gwabza fada, yayin da Isra’ila ta shafe daren jiya tana harba makamai zirin Gaza.  (Saminu Alhassan)