logo

HAUSA

An bude taron shekara-shekara na bankin duniya da asusun IMF a Morocco

2023-10-10 10:42:38 CMG Hausa

An bude taron shekara-shekara na asusun ba da lamuni na IMF da bankin duniya a jiya Litinin, a birnin Marrakech dake kudancin kasar Morocco. A cewar kamfanin dillancin labarai na Morocco wato MAP, taron zai gudana ne har zuwa ranar Lahadin karshen mako, ana kuma fatan zai hallara sama da mutane 12,000, ciki har da tawagogi 190 karkashin ministocin kudi, da manyan bankunan kasashe daban daban, da kusoshin sassa masu zaman kansu.

Rahotanni na cewa, wannan ne karon farko da ake gudanar da taron a wata kasa ta nahiyar Afirka cikin shekaru 50 da suka gabata. Yayin taron na wannan karo, IMF zai fitar da matsayarsa game da ci gaban tattalin arzikin duniya na shekara, kana za a tattauna game da muhimman kalubalolin da duniya ke fuskanta, ciki har da matsalar makamashi, da sauyin yanayi, da rikice-rikicen yankuna, da farfadowa bayan annoba, da nazarin hanyoyin magance matsalolin musamman a kasashe masu tasowa.

An amince da gudanar da taron a Morocco ne bayan da asusun ba da lamuni na IMF da bankin duniya, tare da mahukuntan kasar suka tattauna, game da ikon birnin Marrakech na karbar bakuncin taron, biyowa bayan mummunar girgizar kasa da ta auku a Morocco, a ranar 8 ga watan Satumban da ya shude.  (Saminu Alhassan)