logo

HAUSA

Wata shawarar dake amfanar daukacin duniya

2023-10-10 20:36:09 CMG Hausa

Najeriya kasa ce da ta fi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, kana muhimmiyar cibiyar ciniki ce a yammacin Afirka. Sai dai duk da haka, kasar ta dade tana fama da matsalar karancin wata babbar tashar jiragen ruwa, inda ake samun ruwan teku mai zurfi. Daga baya, a farkon wannan shekarar da muke ciki, an fara amfani da tashar jiragen ruwa ta Lekki, wadda wani kamfanin kasar Sin ya gina, wanda hakan ya kawo karshen wannan mawuyacin halin da Najeriya ke ciki. Ana kuma sa ran ganin wannan sabuwar tasha ta samar da kudin shiga da zai kai dalar Amurka biliyan 360, da guraben aikin yi dubu 170, ga Najeriya. To, idan mun duba sauran kasashen Afirka, gami da na duniya baki daya, za mu iya ganin dimbin misalan da suka yi kama da tashar jiragen ruwa ta Lekki, inda hadin gwiwar da aka yi tare da kasar Sin ke haifar da damammakin samun ci gaban tattalin arziki.

Ko me ya sa hadin gwiwa da Sin ya ke samar da hakikanin ci gaba? Dalili shi ne, kasar Sin tana da wani tsari mai muhimmanci na hadin gwiwa da sauran kasashe, da ake kira shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. A yau ne kuma, ofishin aikin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani, wadda ta bayyana sakamakon da shawarar ta haifar cikin shekaru 10 da suka gabata, da gudunmowarta ta fuskar kare zaman lafiya da tabbatar da ci gaban duniya.

A shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ra’ayi na “Gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan mabambantan al’ummu, da ba su damar cimma moriya da ci gaba tare. Ban da haka, shugaban ya yi amfani da sunayen wasu hanyoyin ciniki da cudanyar al’adu guda 2 masu muhimmanci a tarihi, wajen kirkiro sunan shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, wadda ya gabatar da ita a matsayin dandalin aiwatar da ra’ayin “Kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”. Sa’an nan ruhin shawarar ya hada da: Tattaunawa bisa daidaito don tabbatar da ganin kowa ya ci moriya, da bude kofa ga duk wanda ke son halarta, maimakon kulla karamin kawance da nufin yi wa wasu saniyar ware. Sauran manufofin da shawarar ta kunsa sun hada da magance cin hanci da rashawa, da kare muhalli, da samun ci gaba mai dorewa, da haifar wa jama’ar kasashe daban daban da hakikanin alfanu, da dai sauransu.

Ko wadannan ra’ayoyi da manufofi suna da amfani? Sai an aiwatar da su, daga baya za a gani. Yadda ake aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya shafi bangarorin hada kayayyakin more rayuwa, da tsare-tsaren gudanar da ayyuka na mabambantan kasashe, gami da tabbatar da zumunta da kauna tsakanin jama’arsu. Bisa wannan shawara, kasar Sin ta kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa fiye da 200 tare da kasashe fiye da 150 da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30, cikin shekaru 10 da suka wuce. Kana a nahiyar Afirka kadai, shawarar ta kai ga gina wata babbar cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afirka ta zamani a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda hedkwatar kungiyar kasashen Afirka ta AU take; da kuma baiwa manoman kasashen Afirka damar fitar da karin kayayyakinsu zuwa kasar Sin don samun karin kudin shiga.

Ban da haka, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta sa kasar Congo Brazaville samun wani babban bankin kasuwanci na kanta, da sanya kasar Zambia samun jarin da yawansa ya zarce dalar Amurka biliyan 2.5, da guraben aikin yi fiye da dubu 10, bisa yankin raya tattalin arziki da ciniki da kasar Sin ta gina a kasar, gami da baiwa mutanen kauyuka 9512 na kasashe 21 dake nahiyar Afirka damar kallon telabijin a gidajensu…

Haka zalika, za mu iya fahimtar salon kasar Sin a fannin gudanar da ayyuka, ta hanyar nazari kan takardar bayani da aka gabatar a wannan karo. Wato, da farko shugabannin kasar za su gabatar da wani nagartaccen ra’ayi ko kuma tsarin aiki, daga bisani dukkan al’ummun kasar za su dade suna kokarin aiwatar da tsarin aikin a kai a kai, inda ba za a gabatar da wani tsarin aiki ba tare da aiwatar da shi ba, kana ba za a manta da burin da aka sanya, da ra’ayin da aka gabatar tun da farko ba. Saboda haka, ana ganin yadda shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta kasar Sin, da ra’ayinta na “Gina al’ummar dan Adam mai makomar bai daya” ke haifar da ci gaba a kasashe daban daban, kana tabbas za a ci gaba da ganin abkuwar haka a nan gaba. (Bello Wang)