logo

HAUSA

Najeriya za ta yaki karuwar Jahilci

2023-09-09 17:04:47 CMG

Gwamnatin Najeriya ta jaddada aniyarta ta kawar da annobar jahilci a kasar, yayin da Najeriya ke bikin ranar ilimi ta duniya na shekarar 2023 da ta fada a ranar Juma'a.

Ministan Ilimi Tahir Mamman ya yi wannan alkawarin ne a wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a ranar Juma'a, don bikin tunawa da ranar, mai taken "Samar da ilimi ga duniya da ke fuskantar sauye-sauye: shimfida ginshikin ci gaban al'ummomi mai dorewa da zaman lafiya."

Mamman ya jaddada cewa kawar da jahilci a Najeriya aiki ne mai fifiko a gwamnatin shugaba Bola Tinubu, inda ya kara da cewa ma'aikatar za ta yi aiki tukuru don ganin an cimma hakan. “Jahilci annoba ce kuma cuta, kuma ba za mu bari a ci gaba da jahilci,” a cewar ministan. (Yahaya)