logo

HAUSA

G20 ta amince da Tarayyar Afirka a matsayin memba na dindindin

2023-09-09 16:55:52 CMG

A yau Asabar ne a taron kolin G20, firaministan kasar Indiya Narendra Modi ya bayyana cewa, kungiyar Tarayyar Afirka ta zama memba ta dindindin a G20.

Modi, a jawabinsa na bude taron, ya gayyaci kungiyar Tarayyar Afirka wadda shugaban kungiyar Azali Assoumani ya wakilta, da ya zauna a teburin shugabannin G20 a matsayin mamba na dindindin.

An fara taron kwanaki biyu na taron kolin G20 karo na 18 a yau Asabar a birnin New Delhi na kasar Indiya.

Kasar Sin ta dade tana goyon bayan kungiyar AU wajen shiga G20, tana mai cewa matakin zai tamaka wa nahiyar yin magana da murya daya kan harkokin kasa da kasa da kuma daukaka matsayinta a duniya (Yahaya)