logo

HAUSA

An yi taro kan hadin-gwiwar Sin da Afirka bisa shawarar “ziri daya da hanya daya” a Habasha

2023-09-09 16:57:16 CMG Hausa

Tawagar kasar Sin dake kungiyar tarayyar Afirka wato AU, ta gudanar da wani taro mai taken murnar cika shekaru 10 da gudanar da hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka bisa shawarar “ziri daya da hanya daya” gami da inganta zuba jari a Afirka a jiya Jumma’a 8 ga watan Satumba a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

Shugaban tawagar kasar Sin dake AU, Hu Changchun ya yi jawabin dake cewa, raya shawarar “ziri daya da hanya daya” tare ya kafa sabuwar alkibla ga hadin-gwiwa da mu’amalar Sin da Afirka, da kafa misali ga raya al’ummominsu masu kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamani. Kawo yanzu, kasar Sin tana zuba jari a wasu kasashen Afirka 52, al’amarin da ya samar da miliyoyin guraban ayyukan yi ga al’ummar Afirka.

A nasa jawabin kuma, memba daga kwamitin AU, Albert Muchanga ya ce, shawarar “ziri daya da hanya daya” muhimmin shiri ne na hadin-gwiwar kasa da kasa. A cewarsa, shawarar ta samu manyan nasarori a shekaru 10 da suka gabata, kuma Afirka za ta ci gaba da hada gwiwa tare da kasar Sin, don samar da makoma mai haske na cin moriyar juna a nan gaba. (Murtala Zhang)